Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce bai damu da jita-jitan da ake yaɗawa ba game da aikinsa.
Wadanda suka sayi ƙungiyar Sir Jim Ratcliffe Ineos ana ta yaɗ jita-jitan suna neman kocin da zai ci gaba da tafiyar da ƙungiyar a ƙarshen kakar da ake ciki.
Ana cewa kocin Ingila Gareth Southgate shi ne zai maye gurbin kocin, sai dai ya ce wannan ba daidai ba ne a rika hada shi da aikin wani.
- Yan Sandan Kano Sun Cafke Matashin Da Ake Zargi Da Yi Wa Wani Mutum Yankan Rago.
- Yansanda sun kama wani malami da sassan jikin ɗan adam a Najeriya
“Kasan ko da yaushe ba a rasa abin fada a Manchester United, jita-jita game da kungiyar, kocinta da ‘yan wasanta,” in ji Ten Hag.
“Mun mayar da hankalinmu kan ci gaban United, muna son United ta riƙa wasa sama da wanda take yi yanzu, ban wani damu ba.”
Masu ƙungiyar suna kallon kocin Wolves Gary O’Neil a matsayin wani zaɓi da United take da shi.