Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami da zai iya ratsa nahiyoyi, wanda ya yi tafiyar mintuna 86.
Makamin shi ne irinsa na farko mafi cin dogon zanzo da aka taɓa yin gwajinsa.
An harba makamin da aka yi wa laƙabi da ICBM, wanda ya yi tafiyar nisan kilomita 7,000 a sama, wanda hakan ke nufin inda a kwance aka harba zai yi doguwar tafiyar da babu makami mai linzamin da ya taɓa yin irinta.
Bayan ya dawo ƙasa, makamin ya faɗa cikin ruwan tekun gabashin ƙasar, kamar yadda ƙasashen Japan da Koriya ta Kudu suka bayyana.
Gwajin – wanda aka yi ranar Alhamis – na zuwa ne a daidai lokacin da ke ƙara samun tsamin dangantaka tsakanin Koriya ta Arewa da maƙwabciyarta ta Kudu.
Amurka ta ce gwajin irin waɗannan makaman ya saɓa wa dookin Majalisar Dinkin Duniya.
Ma’aikatar tsaron koriya ta Kudu ta ce gwajin wani yunƙurin Koriya ta Arewa ne ƙara ƙarfafa makamanta.
Cikin wani jawabi da ba kasafai yake irins a gidan talbijin na ƙasar, Shugaban Koriya ta Arewar, Kim Jong Un ya ce gwajin na cikin atisayen soji d ƙasar ke yi, kuma tauna tsakuwa ne kan yadda “za mu mayar da martani kan maƙiyanmu”.