Sojojin Koriya ta Kudu sun ce sama da dakaru ashirin daga Koriya Ta Arewa ne suka tsallaka kan iyakarta da safiyar Talatar nan.
Nan take suka ja da baya bayan da sojojin Koriya ta Kudu suka yi harbin gargaɗi.
Seoul ta ce Koriya ta Arewa na aika dakaru masu yawa zuwa yankin, domin kawar da ciyayi da suka mamaye da kuma dasa nakiyoyi.
An samu faruwar irin wannan lamari a farkon wannan watan.
Dama dai iyakar ƙasashen biyu ba a gine take ba sannan kuma allunan alamar da ke nuni da iyakokin sun ɓace a cikin ciyayi.