Kotu a jamhuriyar Nijar ta cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya

Spread the love
Bazoum

Kotu mafi girma a jamhuriyar Nijar ta cire wa tsohon shugaban Ƙasar, Mohamed Bazoum rigar kariya abin da ke nufin cewa zai iya fuskantar shari’a.

Matakin ya nuna cewa Bazoum zai fuskanci tuhuma a kotun sojin Ƙasar.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar wanda aka kifar da gwamnatinsa a shekarar da ta wuce, yana fuskantar ɗaurin talala, tun bayan da sojoji suka ƙwace iko.

Ana zargin Bazoum da cin amanar kasa da tallafawa ta’addanci da kuma yi wa tsaron kasar zagon kasa.

A makon da ya wuce ne lauyoyinsa suka janye daga karar.

Daya daga cikin lauyoyin ya ce an ki barinsu su gana da Bazoum tun da aka soma batun shari’a kan rigar kariyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *