Kotu ta ƙi amincewa da belin Nnamdi Kanu

Spread the love

Mai sharia’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata, ta ki amincewa da belin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

Sai dai kotun ta bayar da umarnin a gaggauta sauraron shari’ar Kanu wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi cin amanar kasa.

Kanu, wanda aka gabatar da shi gaban kotu a ranar Talata, yana tsare ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan kama shi a watan Yunin 2021 domin yanke hukunci kan neman belin sa.

Nyako ta ce kotun za ta bayar da damar ci gaba da sauraron shari’ar ne kawai, sannan ta umarci masu gabatar da kara da su gabatar da shaida na farko.

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya nuna rashin jin dadinsa da hukuncin.

Kotu ta kori ƙarar lauyan Nnamdi Kanu kan ‘yan sanda da DSS

Kano: Hukumar KNUPDA Ta Bijirewa Umarnin Kotu Kan Yin Rusau A Garin Gurungawa

Ya ce ƙungiyar lauyoyin Kanu ba za ta iya ci gaba da shari’ar ba idan ba a ba su damar yin magana da wanda suke karewa ba.

Ejimakor ya kara da cewa ganawa da Kanu a hannun DSS abu ne mai matuƙar wahala, domin kullum ana sa ido a kan hirar su, kuma Kanu na sanye da irin kayan da kotu ta ce a canza masa.

Ya yi zargin an yi wa Kanu rashin adalci, wanda a cewarsa ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya nuna rashin gamsuwar tawagar lauyoyin Kanu, sannan ya bukaci a dakatar da shari’ar don ba su damar tuntubar wanda yake karewa, wanda kotu ta amince.

Kanu ya nemi ya yi magana a kotu kuma an amince da bukatarsa.

Ya shaida wa kotun cewa yana fama da ciwon zuciya kuma ba ya samun kyakkyawar kulawa a hannun hukumar DSS.

Ya nemi a kai shi gidan yarin Kuje ko kuma a ɗaure shi a gida amma mai shari’a Nyako ta ƙi amincewa da rokonsa wanda daga bisani ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 17 ga Afrilu, 2024 don fara shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *