Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Mawaƙi Kan Hana BBC Amfani Da Kiɗansa

Spread the love

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, karkashin mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ta ki amincewa da bukatar mawaki, Abdul Kamal kan dakatar da BBC daga amfani da kiɗansa.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda wani mawaki a Kano, mai suna Abdul Kamal, ya kai karar Sashen Hausa na BBC kan amfani da kiɗansa a shirin “Daga Bakin Mai ita” ba tare da izininsa ba.

Lauyan mai kare wadanda ake kara, Barista Shakiruddeen Mobuluwaji, ya shaida wa kotun cewa har yanzu lauyan mai kara bai amsa karar da suka ɗaukaka ba.

Kotu ta yanke wa matashin da ta samu da laifin fashin wayar daliba hukunci a Kano

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya koma APC

Lauyan masu kara, Barista Bashir Ibrahim, ya bayyana cewa tuni suka mayar wa da lauyoyin wadanda ake kara martanin da ya dace.

Alkalin kotun mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ya bukaci bangarorin da ake shari’ar da su, su tabbatar da martani kafin ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga Maris, 2024.

Idan ba a manta ba mawakin ya maka BBC a kotu kan cewar suna amfani da sautinsa, ba tare da sun nemi izninsa ba.

Hakan ya sanya kotun dage zaman a baya zuwa 12 ga watan Fabrairu, 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *