Kotu ta ba da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa kan miliyan 10

Spread the love

Wata kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da belin mutum 10 da ake tuhuma da cin amanar ƙasa yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ce ya ba da belin maza tara da mace ɗaya, waɗanda ba su amsa tuhumar da ake yi musu ba kan naira miliyan 10 kowannensu.

Cikin tuhume-tuhumen da ake yi musu har da haɗa baki wajen tunzira sojoji su kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.

Sai dai tun da farko masu shigar da ƙara sun nemi kotun ta yi watsi da neman belin a makon da ya gabata.

Waɗanda ake zargin na iya fuskantar hukuncin kisa idan aka kama su da aikata laifukan da ake tuhumar su.

Alƙalin ya ɗage cigaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 27 ga watan Satumba. Sai dai ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta nemi gwamnati ta sake su ba tare da wani sharaɗi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *