Kotu ta bai wa Abba Kyari beli na mako biyu

Spread the love

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda a Najeriya DCP Abba Kyari na tsawon mako biyu.

Kotun ta ce ta bayar da belin nasa ne domin ba shi damar zuwa gida domin ta’aziyyar mahaifiyarsa wadda ta rasu.

Kotun ta bayar da belin ne kan kuɗi naira miliyan 50 da kuma wani wanda zai tsaya masa.

Haka nan kotun ta ajiye ranar 31 ga wannan wata na Mayu domin sauraron takardar da Abba Kyarin ya shigar na neman beli.

Mahaifiya Abba Kyari ta rasu ne a farkon wannan wata.

Ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare Kyari, Barista Hamza Nuhu Ɗantani ya bayyana wa BBC cewa tuni dama suka gabatar da buƙatar belin nasa a kotu.

Ana tuhumar Kyari ne da laifukan da suka jiɓanci safarar ƙwaya bayan kamen da Hukumar yaƙi da safarar ƙwaya ta Najeriya NDLEA ta yi masa shekara biyu da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *