Kotu Ta Bai Wa DSS Damar Tsare Wani Dan ISIS’ Tsawon Kwanaki 60

Spread the love

Babbar kotun tarayya a Abuja ta bai wa hukumar tsaron farin kaya ta DSS izinin ta ci gaba da tsare wani, Emmanuel Osase, wanda ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar ISIS.

A wani hukunci da Mai shari’a Inyang Ekwo ya yanke, ya bai wa hukumar tsaron damar su ci gaba da tsare Emmanuel Osase a wurinta tsawon kwana 60 don ta kammala bincike kan zargin alaƙarsa da ƙungiyar, wadda hukumomi suka ce ta ‘yan ta’adda ce.

Umarnin tsarewar ya zo ne bayan wata buƙatar wucin gadi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gabatar ta hannun lauyoyinta, A.A Ugee.

Daga bisani kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 3 ga watan Yuni.

Jaridar Vanguard ta ambato takardu kotu na cewa an kama Emmanuel Osase ne saboda tallafa wa ISIS ba kawai wajen yayata saƙonninta ba, da kushe tsarin mulkin dimokraɗiyyar Najeriya, har ma da kiran a kai hare-haren ta’addanci kan Najeriya da al’umominta da ‘yancin kasancewarta ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *