Kotu ta bai wa EFCC izinin rufe asusun banki 1146

Spread the love

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin alƙali Emeka Nwite ta bai wa hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta’annati izinin rufe asusun bankuna 1146 mallakin mutane da kamfanoni da ake gudanar da bincike a kansu saboda zarginsu da hada-hadar kuɗin waje ba bisa ƙa’ida ba da halasta kuɗin haram da tallafa wa ta’addanci.

Alƙalin ya umarci a rufe asusun bankunan har zuwa lokacin kammala bincike.

Da aka yanke hukuncin kan ƙarar da lauyan EFCC, Ekele Iheanacho ya shigar, alƙalin ya ce binciken da za a gudanar zai ɗauki kwana 90.

Alƙalin ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa asusun bankunan na da alaƙa da mutanen da ke amfani da manhajojin musayar kuɗi na kirifto wajen durƙusar da darajar naira.

Alƙalin ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar alkinta kuɗaɗen a asusun bankunan da aka gano har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan lamarin.

Alƙalin ya kuma ɗage ƙarar zuwa 23 ga watan Yulin 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *