Kotu ta bayar da belin Dani Alves

Spread the love

Wata kotu a Sifaniya ta bai wa tsohon ɗan wasan kwallon kafa na Brazil, Dani Alves beli daga gidan yari, har sai an yanke hukunci kan karar da ya ɗaukaka kan hukuncinɗaurida kotun ta yanke masa.

An yankewa tsohon ɗan wasan na Barcelona da Paris St Germain hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da rabi a gidan yari a watan da ya gabata bisa samunsa dalaifin yi wa wata mata fyaɗe a wani gidan rawa da ke birnin Barcelona a watan Disamban shekara ta 2022.

Kotun ta buƙaci Alves ya biya belin Yuro miliyan ɗaya tare da mika fasfo ɗin sa, zai kuma rika gabatar da kansa a gaban kotu a kowane mako.

Majalisa Za Ta Gayyaci Emefiele Kan Bashin N30trn Da Gwamnatin Buhari Ta Karɓa

Sunan Tukur Mamu Ya Fito Cikin Mutane 14 Ma su Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *