Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

Spread the love

Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya, ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi takardun kadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

Wannan mataki dai na nufin kotun ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan yake nufi a kowanne lokaci za a iya kama shi.

Barista Ahmad Musa Umar shi ne lauyan da ke kare Dr Idris, ya ce “kotu za ta iya bai wa ‘yan sanda takardar kama Dakta Idris a kowanne lokaci”.

“Kotun ta ce ta ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami’an tsaro sukai mata shi gabanin wannan rana,” in ji Barista Ahmad Musa.

Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, na farko kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

Na biyu kuma ana tuhumarsa da laifin tayar da zaune tsaye.

Har yanzu dai ba a fara sauraran wannan shari’a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.

Amma a baya ya yi zaman gidan kaso kan waɗannan tuhume-tuhume na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli, in ji lauyansa.

One thought on “Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

  1. Ni Anawa shawara da zambada Ayi binciken kwalwarsa,

    sai kuma Adakatarda shi daga cinmutuncin mutane bawai Adakatarda shi wa’aziba wannan Haqqin Allah ne,

    Abima masu haqqi haqqinsu idan yaci haqqi,

    kuma Ayi Abinda kada yazama yabiyo hukuma Haqqi Akai Akiyaye da wannan,

    Agaya masa yamai da hankali wajen kiran Al’umma dahikima kada yazama yana sukar duk wanda yagadama yasoka,

    Daga Alhaji Aminu Tahir illela ta jahar sokoto state.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *