Kotun magistiri mai namba 80 dake zaman ta a Kano, ta aike da matasan da ake zargi da aikata laifin kisan kai zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.
Jami’an yan sandan ne suka kama matasan da suka hada da, Aliyu Adamu mazaunin unguwar Gaida, Mubarak Adamu Mandawari da kuuma Sadik Sunusi Mandawari, bisa zarginsu da halaka Dahiru Musa Dorayi ta hanyar bashi guda sannan suka kona Gawarsa.
An karanto mu su kunshin tuhumar hadin baki don aikata laifi da kuma kisan kai wanda ya saba da sashi 97 da 221 na kundin Penel code, kuma an karanto mu su.
Lauyar gwamnatin jahar Kano Hajia Binta Bashir, ta shaida wa kotun cewa sabuwar takaddar tuhuma ce.
Tunda farko jami’an sandan sun kama su ne bisa zargin kashe Dahiru Musa, bayan sun gayyace shi zuwa gidan wanda ake zargi na farko a unguwar Gaida, har suka yi masa karyar cewar wani ne zai siyi filotinsa, amma sun yi hakanne don su samu takaddun fili, inda suka sanya masa guda a cikin abinci har ya mutu, sannan suka Kona Gawarsa.
Alkalin kotun mai shari’a Muhammed Alhaji Isah, ya aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 24 ga watan Oktoban 2024.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Sabunta Sashin Karbar Korafin Mutanen Da Jami’in Dan Sanda Ya Ci Zarafinsu.
- Ana Zargin Wani Matashi Da Cinnawa Kakarsa Wuta A Jigawa.