Hukumar HIsaba ta Jihar Kano ta ce kotu ta bayar da umarnin a buɗe asusun ajiyar bankinta da aka rufe a kwanakin baya.
Cikin wata sanarwa da maimagana da yawun Hukumar Auwalu Ado Sheshe ya fitar ta ce, an bude asusun ne bayan da Banban Kwamandan Hisbah Sheikh Aminuddeen Ibrahim Daurawa ya umarci Babban Daraktan hukumar Alhaji Abba Sa’id Sufi da ya nemi ba’asi akan dalilin rufe asusun Bankin hukumar.
Ba tare da ɓata lokaci ba, babban daraktan ya tuntubi ma’aikatar shari’a domin samun shawarwari akan lamarin.
A wata hira da ya yi da manema labarai, Aminuddeen Daurawa ya ce “an samu kuskure ne, umarnin kotun cewa ta yi a rufe asusun namu na iyakar kuɗi da ba za su shiga ba, ma’ana duk abin da ya haura dubu 800 ba zai fita daga asusunmu ba,” in Daurawa.
Daga baya aka buɗe wa Hisba asusun, tare da neman afuwar da bankin ya yi ga hukumar.
Jami’ai a Chile sun ce gobarar daji ta halaka mutum aƙalla 51
Kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo, Daurawa ya ce an rufe asusun Hisbah ne sakamakon wani sumame da hukumar ta yi a wani otal dake Sabon Gari a shekarar 2019, kan haka kungiyar masu Otal suka gurfanar da hukumar a gaban kotu, in sanarwar.
Sanarwar hukumar ta ce duk da wannan matakin da aka ɗauka kanta, ba zai kashe mata gwiwa ba wajen gudanar da aikinta na umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.