An sake Gurfanar da matashinnan, Mai suna Shafi’u Abubakar, a gaban babbar Kotun Shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Rijiyar Zaki Kano, bisa Zarginsa da cinnawa masallata.
A zaman Kotun na ranar Laraba, lauyan Gwamnatin jahar Kano, barista Salisu Mohammed Tahir, ya rokon kotun ta ba wa Dagacin Garin da lamarin ya Faru, umarnin gayyato wasu shaidu guda biyu don bayar da shaida kan Zargin da ake Yi wa Wanda ake kara.
Lauyar dake kare Wanda ake Zargin barista Hasiya Muhd Imam, ba ta Yi suka ba kan rokon.
IDONGARI.NG, ta ruwaito cewa lauyoyin dake gabatar kara sun niyyar Jin shaidunsu a wannan rana da kotun ta Sanya don ci gaba da sauraren Shari’ar, sai dai ragowar shaidun 2 ba su samu damar zuwa ba.
Haka zalika lauyan Gwamnatin jahar Kano, ya shaida wa kotun cewar , akwai Wani jami’in Dan Sandan da ya gudanar da bincike.
Saboda haka ne muka roki Kotun ta Sanya mana wata rana don karasa gabatar da shaidun mu.
” Fatan mu shi ne wadannan shaidu na mu kamar yadda suka je suka bayar da bayanan abunda ya Faru ga jami’an Yan Sanda haka muke so su ba wa Kotu domin adalci Ake so” Lauyan Gwamnatin Kano “.
Lauyan Gwamnatin ya ce dalilin ya sa , suka roki Kotun ta aikawa Dagacin Takaddar da kanta shi ne, saboda mutanen Garin sune masu hakki.
Anata bangaren lauyar dake Wanda Ake Zargin, barista Hasiya Muhd Imam, ta ce fatan shi ne Kotu ta Yi adalci.
Idan ba a manta ba IDONGARI.ng, ta ruwaito cewa ana zargin Shafi’u Abubakar, da zuba Fetur a cikin Wani masallaci sannan ya cinna wuta, Inda masallata sama da 20 suka rasu.
Mai Shari’a Halhalatul Kuza’i Zaariyya, ya dage ci gaban Shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba 2024.