Kotu Ta Dage Sauraren Da’awar Makarantar Imamu malik Kan Zargin Siyar Da Filin Da Mallam Ibrahim Shekarau Ya Ba Su.

Spread the love

 

Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Shahuci kano, ta dage sauraren gabatar da Da’awar da makarantar Imamu Malik Bin Anas dake ungwar Sabuwar gandu karamar hukumar Kumbotso, ta shigar bisa zargin siyar mu su da filin makarantar da tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau, ya basu a matsayin Wakafi don gina makarantar da za a dinga koyar da yara karatun alkur’ani mai girma.

Kotun ta dage sauraren da’awar masu kara ce, saboda akwai mutum daya da ba a sadashi da sammaci ba, kuma a tsari na shari’a babu yadda za a gabatar da da’awa ba tare da daya daga cikin sassan shari’ar bai san ana kararsa ba, shi yasa kotun ta dage zaman don yi wa kowanne bangare adalci.

Lauyan ma su kara, Barista Usaini Makari, ya bayyana cewa daman sun shigar da karar kan wakafin da tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, mallam Ibrahim Shekarau, ya yi wa makarantar dan Yara su yi karatun alkur’ani, amma sai suke zargin wasu mutane sun siyar da wajen tare da tarwatsa daliban, don haka suke son kotu ta dawo musu da wajensu.

Wadanda aka yi karar sun hada da tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau, Haruna Shekarau, Salisu Lawan Indabawa, Dahiru Shekarau , Sani Adamu, Tahir Yusuf da dai sauransu.
Alkalin kotun mai shari’a Mallam Muhammad Sani Ibrahim, ya dage shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Janairun 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *