Kotu ta dakatar da ƴansanda tilasta neman izinin sanya gilashin mota mai duhu

Spread the love

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Warri da ke jihar Delta, ta bayar da umarnin wucin gadi na hana sfeton ƴansandan Najeriya tilasta neman izini ga masu motocin da ke sanya gilashinsu ya yi duhu.

Umarnin ya kuma hana jami’an ƴansanda aiwatar da dokar da rundunar ta sanar wadda ta ce zai fara aiki daga ranar Litinin 6 ga watan Oktoba, 2025.

A yayin da yake bayyana hukuncin kotun, mai shari’a Hyeladzira Nganjiwa ya amince da buƙatun mai shigar da ƙarar na hana waɗanda ake ƙarar da suka haɗa da ƴankwangila ko diloli da shugaban ƴan sanda da jami’anta yin komai a kan dokar har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotun.

Haka zalika umarnin ya hana ƴansanda tsayar da wasu, ko cin zarafinsu ko tsare su ko motocinsu a ƙarƙashin dokar.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Oktoba, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *