Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano, majalissar dokoki kan nada Kantomomi

Spread the love

Babbar Kotun tarayya dake zamanta a jihar Kano dake Arewacin Nigeria ta dakatar da gwamnatin jihar Kano da Majalisar dokokin jihar nada ko tabbatar da nadin Kwamitocin riko na shugabannin kananan hukumomin jihar wanda za su maye gurbin zababbun shugabannin kananan hukumomin da wa’adinsu ya kare.

Kotun ta bada umarnin ne bayan wani rokon gaggawa da aka shigar a gabanta da ya bukaci dakatar da nadin har sai an saurari karar dake gabanta.

Herbert Wigwe ya taimake ni bayan an sauke ni daga sarkin Kano

An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi don cire dala miliyan 6.2 a CBN’

Alkalin Kotun justis A. M. Liman da ya bada umarnin ya ce kowanne bangare ya tsaya a matsayin da yake har sai an saurari karar dake gabanta wacce Haruna Abbas Babangida ya shigar ta hanun lauyansa Barista Abdul Adamu.

Kotun ta kuma bada umarnin a kaiwa dukkan bangarorin da ake Kara a shari’ar hukuncinta ta hanun kowanne irin ma’aikaci a ma’aikatar shara’a ta jihar Kano.

Kotun ta dage sauraron shara’ar zuwa ranar 14 ga watan Maris, 2024.

Globaltracker

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *