Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) karbar Miliyan10 da Miliyan 5 daga hannun ‘yan takarar shigabanci ƙaramar Hukumomi da kum Kansiloli a zaben kananan hukumomi da ke tafe.
Alkalin kotun mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba.
SolaceBase ta ruwaito cewa Action Peoples Party (APP) , Action Democratic Party (ADP) da Social Democratic Party (SDP) ne suka shigar da karar Kotu.
Sai dai wanda ake tuhuma a cikin lamarin shi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano.