Kotu Ta Daure Matashi Wata 6 Kan Satar Magi Da Sabulu

Spread the love

Wata kotu da ke zamanta a Jihar Filato ta yanke wa wani matashi mai shekaru 22 hukuncin daurin watanni shida a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, bisa samun sa da laifin satar kwalin magi da kuma kwalin sabulu wadanda kudinsu ya kai N55,000.

Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa tare da rokon kotun da ta yi masa sassauci.

Ta kuma bai wa mai laifin zabin biyan tarar N20,000.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa wani Mista Gbenga Ayantola ne ya kai kara ofishin ’yan sanda na “A” a ranar 10 ga watan Oktoban 2023.

Ya ce wanda ake tuhumar ya kutsa cikin shagonsa inda ya saci katon na magi da kuma sabulun wanka wadanda kudinsu ya kai N55,000.

Dan sandan ya shaida wa kotun cewa a lokacin da ’yan sanda ke gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

Ya ce laifin ya ci karo da dokar ‘Penal Code.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *