Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta gaza zaman sauraron ƙarar da hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa ta shigar don ƙalubalantar umarnin wata babbar kotu a Kogi da ta hana ta kama tsohon gwamna Yahaya Bello.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa kotun ta Kogi a hukuncinta na ranar 17 ga watan Afrilu, ta dakatar da EFCC daga kamawa ko tsarewa ko kuma tuhumar Yahaya Bello.
Alƙali A.A Jamil ne ya bayar da umarnin ranar Laraba a wani hukunci da aka shafe sa’a biyu ana yi a Lokoja, babban birnin jihar ta Kogi.
Hukuncin ya zo daidai da samamen da jami’an EFCC suka kai gidan Yahaya Bello da ke Abuja a wani yunƙurin cafke shi.
EFCC na neman gurfanar da tsohon gwamnan kan zargin aikata laifuka 19 da suka shafi halasta kuɗin haram da cin amana da kuma karkatar da kudin da ya kai naira biliyan 80 da ɗoriya.
EFCC dai na son Bello ya fuskanci shari’a saboda laifin da ake zargin ya aikata abin da ya sa ta shigar da ƙara gaban kotun tarayya a Abuja domin samun izinin kama shi