Wata Babbar Kotu a Kano ta umarci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya daina bayyana kansa a matsayin sarki.
Umurnin kotun ya kuma shafi sauran sarakuna guda hudu da gwamnatin Kano ta tube wato na Rano da Gaya da Bichi da Karaye.
Gwamnatin Kano da majalisar jihar ne suka shigar da karar, kuma a lokacin da take zartar da hukunci, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da ikon majalisar jihar kan sauke sarakunan da kuma ikon gwamna na tabbatar da dokar.