Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, gyaran Fadar Nassarawa.
Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Babban Lauyanta da kuma Masarautar Kano ne, suka maka Aminu Ado Bayero a kotu.
Kotun ta bayar da umarnin cewa dukkanin ɓangarorin da ke cikin wannan shari’a su bar komai yadda yake game da tsarin ginin fadar har sai an saurari ƙarar tare da yanke hukunci.
Umarnin kotun ya ce: “An bayar da umarnin wucin gadi na hana wanda ake ƙara, wakilansa, ko duk wanda ke aiki bisa umarninsa daga rushe, gyarawa, ko sake gina Gidan Sarki na Nassarawa da ke kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano, har sai an saurari wannan ƙara tare da yanke hukunci.”
Takardun kotun wadda wakilinmu ya gani, ta nuna cewa masu ƙara sun shigar da ƙarar ne a ranar 9 ga watan Satumba.
Ƙarar mai sakin layi 33 da Matawallen Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed, ya sanya wa hannu
Kotu ta kuma bayar da umarnin a kai wa Sarkin takardun kotu ta wata hanya ta daban, tare da tsayar da ranar 2 ga watan Oktoba domin sauraron ƙarar.
- Tinubu ya jinjina wa sojojin Najeriya kan kisan Halilu Sububu
- Kwale-kwala ya kife da mutum fiye da 40 a Zamfara