Mai shari’a Joyce Abdulmalik na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya umarci babban bankin Najeriya CBN da ya dakata da bai wa jihar Rivers kasonta daga asusun gwamnatin tarayya na wata-wata.
Mai shari’a Abdulmalik ya ce kuɗaɗen kason da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara yake karɓa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya saɓa doka, kuma dole a dakatar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Alƙalin ya ce gabatar da kasafin kuɗin da gwamna Fubara ya yi a gaban ƴan majalisar jihar guda huɗu kacal ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Wannan ya sa alƙalin ya buƙaci babban bankin Najeriya da akanta-janar na ƙasar da bankin Zenith da bankin Access da su tabbatar Fubara bai ci gaba da amfani da kason jihar na wata-wata ba.