Kotu ta haramta bincike kan Ganduje game da bidiyon dala

Spread the love

Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar ba ta da ikon ta gayyaci ko ma ta gudanar da bincike kan tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje game da bidiyon dala.

Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ne ya yanke hukuncin ranar Talata a ƙarar da Ganduje ya shigar kan hukumar ta PCACC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje ya shigar da ƙarar a watan Yulin 2023 inda ya nemi a kare masa ƴancinsa bayan da shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya gayyace shi da ya bayyana domin amsa tambayoyi kan bidiyon dala.

Kotun ta ba da umarnin hana gayyata ko kuma bincikar Ganduje har sai abin da kotu ta tsayar a ƙarshe.

A 2018 ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a lokacin da Ganduje yake gwamna, bidiyon ya nuna shi yana karɓar damun daloli daga hannun wani ɗan kwangila.

EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abinci

Ba mu da niyyar yin katsalandan a dimokraɗiyyar Najeriya – Janar Lagbaja

Sai dai Ganduje ya musanta zargin inda ya ce haɗa bidiyon aka yi.

Lauyan hukumar ta karɓar ƙorafe-ƙorafe, Usman Fari ya ce ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin kotun ta yanke hukunci a ƙarar da aka shigar tun Yulin bara inda ya ce tuni ya samu izinin wanda yake ƙarewa domin ɗaukaka ƙara.

Lauyan Ganduje, Mathew Burkaa mai mukamin SAN ya ce hukuncin kotun ya tabbatar da matsayinsa cewa hukumar ba za ta iya yin bincike kan wanda yake karewa ba kan wata doka da ke ta tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *