Kotu ta haramta dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga APC

Spread the love

Wata babbar kotun tarayya a Kano ta dakatar da shugabannin jam’iyyar APC a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa daga ɗaukan ƙarin mataki a kan dakatar da shugaban jam’iyyar ta ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

A wata takardar kotu mai ɗauke da sa hannun magatakardan kotun, Usama Ibrahim Isah, mai shari’ar Abdullahi Muhammad Liman ne ya bayar da umarnin inda ya buƙaci mutanen da ake ƙara da su guji aiwatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da shugaban APC ya shigar a kotu.

Umarnin kotun ya zo ne sa’oi bayan da babbar kotu a Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje saboda zarginsa da rashawa.

Kotun ta kuma umarci ɓangarorin da su tsaya kan matsayin da ake kafin taron manyan jam’iyyun APC na mazaɓar ta Ganduje wanda bayansa ne aka dakatar da shugaban jam’iyyar a mazaɓar.

Mai shari’a Liman ya sa ranar 30 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a saurari shari’ar.

Waɗanda ake ƙara sune Haladu Gwanjo da Nalami Mai AC da Muhammadu Baiti da Danmalam Gata da Musa Lado da Laminu Sani Barguna da Umar Sanda da Auwalu Galadima da Abubakar Daudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *