Kotun ɗaukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da Felix Okonkwo lauyan da ke kare Nnamdi Kanu, jagoran masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) da ake tsare da shi ya shigar kan zargin kama shi da tsare shi da ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya suka yi ba bisa ka’ida ba.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Okon Abang ya yi watsi da ɗaukaka karar, inda ya bayyana cewa ba shi da inganci.
Ya yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya kasa nuna rashin adalci a hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan lamarin.
Abang ya jaddada cewa, hujjojin bidiyon da masu karar suka gabatar a lokacin shari’ar ba su nuna wani hannun jami’an DSS ba a wurin da aka kama su a gidan Ifeanyi Ejiofor a jihar Anambra.
Dangane da diyyar naira miliyan biyu da aka ce ƴandan da DSS su bayar, mai shari’a Abang ya ki amincewa da hujjar wadanda suka shigar da kara na cewa adadin kuɗin bai wadatar ba, inda ya ce hurumin tantance diyya ya rataya a wuyan alkali ne kawai.
Kano: Hukumar KNUPDA Ta Bijirewa Umarnin Kotu Kan Yin Rusau A Garin Gurungawa
Sojoji sun kuɓutar da mutum 16 da ƴanbindiga suka sace a Kajuru
Bugu da kari, Mai shari’a Abang ya lura cewa wadanda suka shigar da ƙarar sun kasa bayar da bayanan da suka dace kamar matsayinsu a al’umma da kuma asarar da suka yi a lokacin da ake tsare da su.
Wadanda suka shigar da karar da suka hada da Felix Okonkwo da Ikenna Chibuike, da Okafor Ugochukwu, sun shigar da karar ne a gaban babbar kotu kan jami’an ‘yan sandan Najeriya da kuma hukumar DSS, inda suke zargin su da take hakkinsu.
Sun zargi jami’an tsaro da kama su da tsare su ba bisa ka’ida ba a watan Satumban 2021, inda suka yi iƙirarin cewa ana azabtar da su da cin zarafinsu da kuma tursasa musu.
A wani hukunci da ya yanke a ranar 24 ga Maris, 2022, Mai shari’a Samaila Bature ya samu ‘yan sanda da laifin kamasu da tsare su ba bisa ka’ida ba tare da ci musu tarar Naira miliyan biyu a kansu.
Sai dai babu wani mataki da aka ɗauka a kan hukumar ta DSS domin wadanda suka shigar da karar ba su gano dalilin daukar matakin a kansu ba.