Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya yi watsi ƙa karar da shugaban IPOB Nnamdi Kanu ya shigar kan gwamnatin tarayya.
Kanu ya kai ƙarar Babban Lauyan Tarayya da Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS, su biya shi diyyar naira biliyan ɗaya bisa zargin tauye masa haƙƙi.
Kanu ya yi iƙirarin cewa hukumar DSS da babban daraktanta sun keta haƙƙin sa na shari’a ta hanyar hana lauyoyinsa ganawa da shi ba tare da wata tangarda ba yayin da ake tsare da shi a shirye-shiryen kare shi kan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
A yayin da yake yanke hukunci, mai shari’a Omotosho, ya bayyana cewa Kanu ya gaza bayar da sahihan hujjoji da za su tabbatar da cewa an yi karan-tsaye wajen ganawa da lauyoyinsa.