Rundunar ‘yan sandan birnin New York za ta biya dala miliyan 17.5, a wani shari’ar da wasu mata Musulmi suka jagoranta, waɗanda aka tilasta musu cire hijabi yayin da aka ɗauki hotonsu.
Shari’ar ta 2018 ta bayar da hujjar cewa Jamilla Clark da Arwa Aziz sun fuskanci cin zarafi na ‘yancin yin addini da kuma ta rayuwa.
Lauyoyi sun ce sama da mutum 3,600 ne suka cancanci a biya su karkashin yarjejeniyar.
Ƴan sanda sun canza tsari shekaru huɗu da suka gabata don ba da izinin sanya hijabi.
Birnin ya ce lamarin ya haifar da sauyi mai kyau.
Dole ne alkali na tarayya da ke sa ido kan shari’ar ya amince da yarjejeniyar biyan diyyar.
Kamar yadda bayanan kotun suka nuna, Ms Clark ta yi kuka tare da rokon a bar ta saka hijabinta yayin da ‘yan sanda suka ɗauki hotonta.
“Lokacin da suka tilasta min cire hijabi na, sai na ji kamar tsirara nake, bani da tabbacin ko kalmomi za su iya kwatanta yadda nake ji da kuma cin zarafina da aka yi,” in ji Ms Clark a wata sanarwa a ranar Juma’a.
- Saliyo ta ayyana dokar ta-ɓaci kan maganin ‘Kush’
- Ana Zargin Kungiyar AOJF Da Siyar Da Shinkafar Da Fatima Dangote Ta Basu Don Rage Radadin Rayuwa.