Kotu Ta Raba Auren Nasir Buba Da Taslim Baba Nabegu Ta Hanyar Kuli’i.

Spread the love

 

Babbar Kotun shari’ar addinin ta Kasuwa, dake zaman ta a Shahuci Kano , kar karkashin jagorancin Mai Shari’a Abdu Abdullahi Waiya, ta raba auren, Taslim Baba Nabegu da kuma mijinta Nasir Buba ( Jalam).

Tunda farko matar ta garzaya gaban kotu ce, Inda ta Yi karar mijinta don Neman saki tunda ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba.

A baya lauyan Nasir Buba, Barista Saluhu Umar Kududdufawa, ya roki Kotun ta juyar da Shari’ar zuwa wata kotun , Inda ya ce kotun ta na Sanya gajeriyar rana duk lokacin da ta dage zaman ta.

A zaman kotun na ranar Juma’a, Wanda Aka Yi karar da lauyan sa Babu wanda ya halacci zaman, kuma babu Wani aike kan dalilin rashin bayyanarsu a gaban kotun.

Alkalin kotun Mai shari’a Malam Abdu Abdullahi Waiya, ya ce sun raina kotun , Inda ta kafa hujjojin yanke hukuncin sakin matar ta hanyar kuli’i, da za ta biya tsohon mijin nata naira Miliyan Daya.

Hukuncin na zuwa ne, bayan Wani Zargi da tsohon mijin ya Yi wa tsohuwar matar tasa , wannan dalili ne ya Sanya, Taslim, garzaya wa gaban kotun domin ta raba auren su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *