Babbar kotun jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta rushe kananan hukumomin mulki 33 da tsohon gwamnan jihar marigayi Oluwarotimi Akeredolu ya kirkiro.
A hukuncin da alkalin kotun, Justice A. O Adebusuoye ya yi a yau Alhamis ya bayyana Kananan hukumomin da cewa ba a kirkiro su bisa doka ba.
Alkalin ya zartar da cewa abu ne da ya saba wa doka, ga gwamna ya sanya hannu a kan wata doka a wajen jiharsa.
Kotun ta kara da cewa dokar da marigayi Akeredolu ya sanya wa hannu ta kirkiro kananan hukumomin a 2023 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta saba wa doka, a don haka ba ta da halarci.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kamfanin dillancin labarai na Najeriya, wato NAN, ya ruwaito cewa a ranar 9 ga watan Satumba na 2023 Akeredolu ya sanya hannu a kan kudurin dokar kirkiro kananan hukumomi 33 a jihar, kudurin da kakakin majalisar dokokin jihar Chief Oladiji Olamide ya gabatar masa a gidan shi tsohon gwamnan da ke Ibadan.