Kotu Ta Sa Ranar Sauraren Rokon Daukaka Kara Kan Hukuncin Kisan Abduljabbar

Spread the love

 

Babbar Kotun Jihar Kano ta fara sauraren bukatar daliban malamin nan Abduljabbar Nasir Kabara na neman daukaka kara kan hukuncin kisa da Kotun Musulunci ta yanke masa.

Mai karar, San Turaki Daki, wanda shi ne shugaban kungiyar As-habul Kahfi, ta hannun lauyansa, Barista Hashim Hussaini Fagge, yana rokon ya daukaka kara don kalubalantar hukuncin kisa ta hanyar rataya da Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu ta yanke wa Abduljabbar Nasiru Kabara – Wikipedia bayan ta same shi da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Fali ya shaida wa kotun cewa ya shigar da rokon ne saboda damar da Sashe na 272 a Kundin Mulkin Kasa na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.

Ƴansanda sun jefa wa masu zanga-zanga hayaƙi mai sa hawaye a Senegal

Kotu ta buɗe asusun bankin Hukumar Hisba ta Kano

Ya kara da cewa ya shigar da wannan kara ne tun a ranar 4 ga watan Satumba 2023.

Yayin da aka saurari karar a yau Litinin, lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barista Musa Dahuru Muhammad ya shigar da wani rokon na nema karin lokaci don yin suka game da rokon masu kara.

Haka kuma lauyan kariya Barista Hashim Fagge ya yi suka inda ya nemi kotun ta ba su kwana bakwai domin su yi suka game da rokon Gwamnatin Jihar Kano din.

Bayan sauraron bangarorin biyu alkalin kotun, Mai Shari’a  Sanusi Ado Ma’aji ya sanya ranar 12 ga watan Fabrairu don sauraren bukatun biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *