Kotu ta samu Bobrisky da laifin wulaƙanta naira

Spread the love

Babbar kotu tarayya da ke Legas ta samu Idris Olanrewaju Okuneye da aka fi sani da Bobrisky da laifin wulaƙanta naira.

Alƙalin ya ajiye ranar yanke wa Bobrisky hukunci zuwa 9 ga watan Afrilu inda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC.

Kafin samun sa da laifi, Bobrisky ya shaida wa kotu cewa ba shi da masaniya kan dokar hana wulaƙanta naira.

Alƙalin ya shaida masa cewa rashin sani ba hujja ba ne a doka.

Bobrisky ya kuma nemi alƙali da ya sake ba shi dama ta yin amfani da shafinsa na sada zumunta wajen ilmantar da mabiyansa game da illar yin liƙi da kuɗi.

“Ina da tarin mabiya fiye da miliyan biyar. Zan ɗora bidiyo a shafina kuma na faɗakar da mutane game da yin liƙi da kuɗi.

“Ba zan sake yi ba, na yi da na sanin abubuwan da nayi.”

Bobrisky dai na iya fuskantar hukuncin wata shida a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 50 ko ma ya yi duka biyun.

A ranar Laraba ne hukumar EFCC ta kama Bobrisky kan zargin wulaƙanta naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *