Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Danbarwar Gyaran Gidan Sarki Na Nasarawa.

Spread the love

 

Wata babbar kotun jihar Kano, ta sanya ranar 10 ga Oktoba 2024, don yanke hukunci kan karar da aka shigar gabanta na neman hana mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado-Bayero gyaran gidan sarki na Nassarawa.

Gwamnatin Jihar Kano da Babban Lauyan Kano da kuma Majalisar Masarautar Kano ne , suka shigar da karar ta hannun lauyansu Rilwanu Umar SAN, wanda ya shigar da karar a ranar 12 ga Satumba 2024.

Masu karar na neman kotu ta hana Alhaji Aminu Ado-Bayero gyara gidan sarki na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin jahar Kano.

Alhaji Aminu Ado-Bayero dai shi ne wanda ake kara.

A lokacin da aka zo sauraron karar, Lauyan ma su kara Habib Akilu, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar ko shi ko wakilansa ba wanda ya halarci zaman kotun.

Akilu ya gabatar da takardar neman shiga tsakani yana neman a hana wanda ake kara sake ginawa ko canza fasalin gidan sarkin na Nasarawa.

A ranar 13 ga watan Satumba 2024, kotun ta bayar da umarnin dakatar da wanda ake kara, da wakilansa, daga rushewa, gyarawa, ko sake gina gidan Sarkin na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar Kano, har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma yanke hukunci a kan Shari’ar.

Kotun ta kuma umurci dukkanin bangarorin da suke cikin karar da su tsaya a yadda suke har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.

Kadaura24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *