Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Danbare, ta sanya ranar 23 ga watan Disamban 2024, don yanke hukunci kan tuhumar da ake yi wa matashinnan mai suna Shafi’u Abubakar, da zargin cinna Wuta a masallaci lamarin da ya janyo rasuwar mutane 23, a garin Larabar Abasawa dake karamar hukumar Gezawa ta jahar Kano.
A ranar 15 ga Mayun 2024, ana tsaka da yin Sallar Asuba wanda ake zargin, ya watsa fetur a cikin masallacin sannan rufe kofa ya cinna wuta, kuma duk kayayyakin cikinsa masallacin sun kone kurmus.
Ana zargin matashin da aikata laifuka hudu da suka hada da kisa, da yunkurin aikata kisa, da samar da mummunan rauni da kuma barnata dukiya wanda hakan ya saba sashe na 140, 148, 167 da 370, inda matashin ya amsa dukkanin laifukan da ake zargin sa aikata wa.
A zaman kotun na yau Talata, lauyan gwamnatin Kano kuma mai gabatar da kara, Barista Salisu Ibrahim Tahir, ya ce daman su, sun gama gabatar da shaidunsu guda 6, kuma an sanya wannan rana ce don lauyar wanda ake tuhuma su gabatar da shaidunsu kamar yadda www.idongari.ng, ta ruwaito .
- Kungiyar Ci Gaban Unguwar Dukawuya Ta Yaba Wa Rundunar Yan Sandan Kano Wajen Dakile Aiyukan Batagari
- Ademola Lookman Ya Zama Gwarzon Dan Kwallon Kafa Na Afirka
Kotun ta tambayi lauyar wanda ake tuhuma, Barista Asiya Imam, inda ta shaida wa kotun cewa ba su da wata shaida, domin wanda ake tuhumar shi ne, zai kare kansa, kuma bayan kotun ta tambaye shi ko yana da shaida nan ta ke ya shaida mata cewa babu kawai dai yana jiran hukuncin kotun.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Malam Halhalatul Huza’i Zakariyya, ya sanya ranar Litinin 23 ga Disamba 2024, don yanke hukunci kan wanda ake tuhuma.