Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Danbare Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mallam Halhalatu Huza’i Zakariya, ta sauya ranar yanke wa matashinan nan mai suna Shafi’u Abubakar, hukunci bisa tuhumar da ake yi masa, da laifin bankawa masallata wuta a garin Gadan dake karamar hukumar Gezawa ta jahar.
Kotun dai ta fara sanya ranar 24 ga watan Disamba 2024, don yanke hukuncin , sai dai kotun ta ce za ta yanke hukuncin ne a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2025.
Lamarin ya Faru ne tun a ranar 15 ga watan Mayu 2024, Inda matashin ya watsa Fetur a cikin masallacin sannan ya rufe kofa ya cinna wuta , kuma duk kayayyakin cikin masallacin suka Kone kamar yadda Jaridar https://Idongari.ng, ta ruwaito.
An Zarge shi da aikata laifuka hudu da suka hada da kisa da Yunkurin aikata kisa, Samar da mummunan rauni da kuma barnat dukiya Wanda ya saba da sashe na 140, 148, 167 da kuma 370 Inda matashin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen.
- Zargin Ta’addanci : Kotu Ta Umarci Ministan Shari’a Da DSS Su Gabatar Da Bodejo A Gaban Ta.
- Morocco Za Ta Samar Da Dokar Da Za Ta Bai Wa Mace Ikon Hana Mijinta Kara Aure