Kotu Ta Tabbatar Da Abure A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Labour

Spread the love

Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake Abuja ya ayyana Julius Abure a matsayin tabbataccen shugaban jam’iyyar Labour.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Nwite ya tabbatar da tsagin da Abure ke yiwa jagoranci da kuma babban taron jam’iyyar daya gudana a garin Nnewi a watan Maris din daya gabata wanda ya samar da shugabancin jam’iyyar na kasa.

Har ila yau, Mai Shari’a Nwite ya umarci hukumar zaben Najeriya (INEC) data amince da Abure a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar, inda ya rushe matsayar hukumar ta baya na cewa shugabancin Abure bai inganta ba.

An ruwaito Nwite na cewar, “ina da ra’ayin cewar kuma haka ala’amarin yake a cikin wadannan sahihan takardu, cewar yunkurin wadanda ake kara na tsige sahihancin shugabanci mai kara bai yi nasara ba.”

“Wanda ake kara ya gamsar da kotu. Don haka nake umartar wadanda ake kara dasu baiwa jam’iyyar masu kara karkashin jagorancin Barista Julius Abure dukkanin hakkoki da alfarmar da ake baiwa jam’iyyar siyasa mai cikakkiyar rijista a Najeriya.”

INEC na jayayya akan cewa babban taron jam’iyyar Labour na kasa ya sabawa kudin tsarin mulkin Najeriya da dokar zabe sannan jam’iyyar ta gaza cika sharudan doka na gudanar da taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *