Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

Spread the love

Wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ga shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Mai shari’a Usman Malam Na’abba ne ya yanke hukuncin bayan ƙarar da Dakta Ibrahim Sa’ad ya shigar a madadin jagororin jam’iyyar biyu a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Kano.

Mambobin jam’iyyar da aka shigar da ƙarar a madadinsu su ne – mataimakin sakatare, Laminu Sani da mai bai wa APC shawara kan harkokin shari’a, Haladu Gwanjo waɗanda suke cikin ƴan jam’iyyar tara da suka dakatar da Ganduje kwanaki biyu da suka gabata.

Kotun ta kuma nemi Ganduje da ya daina ayyana kansa a matsayin mamba a jam’iyyar ta APC.

Mai shari’a Na’abba ya dakatar da kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC a Kano da ya guji yin katsalandan kan matakin shugabannin jam’iyyar a mazaɓar Ganduje da kashi biyu bisa uku na galibin shugabannin jam’iyyar suka sa hannu a kai kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada.

A baya-bayan nan ne wasu shugabannin APC tara a mazaɓar ta Ganduje suka ce sun ɗauki matakin dakatar da Ganduje bayan wata takardar koke da wani ɗan jam’iyyar Ja’afaru Adamu ya shigar.

A takardar koken, Adamu ya yi magana kan tuhume-tuhumen rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan inda ya buƙaci jagororin mazaɓar su gudanar da bincike kan batun domin farfaɗo da ƙimar jam’iyyar da kuma tasirin da batun zai yi a fafutukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yaƙi da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *