Kotu Ta Tsare Matashin Da Ake Zargi Da Satar Kayayyakin Miliyoyin Naira A GSS Kwankwaso

Spread the love

Kotun shari’ar addinin addinin musulinci dake zamanta a unguwar Gama PRP Kano, ta bada umarnin tsare wani matashi mai suna Usaini Sulaiman Unguwa Uku, bisa zarginsa da aikata laifin shiga talaifi, yin sata da samunsa da kayan sata, wanda hakan ya saba da sashi na 120, 215, 133 da 198 na kundin SPCL.

Ana zargin matashin da shiga makarantar sakandiren Garin Kwankwaso a ranar 7 ga watan Oktoba 2023 da misalin karfe 4:00am ,inda yayi awon gaba da kayayyaki masu tarin yawa.

Tunda fari daya daga cikin Malaman makarantar GSS Kwankwaso ne ,mai suna Jazuli Baba Ali, ya yi korafi da cewar wanda ake zargin ya sace baturan sola guda 2 masu kimar kudi naira 300, Penal na sola guda biyu masu kimar kudi naira dubu 240, Moniton na’ura mai kwakwalwa guda 4 mai kimar kudi dudu dari 200 , CPU masu kimar kudi dubu 20 da kuma Somon Sola masu kimar naira dubu dari 535.

sauran kayayyakin sun hada da Na’ura mai kwakwalwa mai kimar kudi naira dubu 150, Fitulu masu kimar kudi naira dubu 7500, man girki na naira dubu 20 , sai kuma kudi naira miliyan biyu da dubu dari uku da talatin da aka sace a ofishin shugaban makarantar, da wata naira miliyan da dubu dari hudu da saba’in da huda da naira dari takwas da talatin da suka yi batan dabo a makarantar.

Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa ,inda nan ta ke ya amsa laifin sace kayayyakin sai dai ya ce bai sace somo ba, amma sauran kayan duk shi ne ya sace su kuma ya siyarwa da wani mai suna Mustapha wasu daga cikin kayan kan kudi naira dubu 122.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *