Wata kotun majistiri karkashin jagorancin mai shari’a Rakiya Lami Sani, ta aike da wani matashi mai suna Adam Mainasara, zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya bisa zarginsa da yunkurin kashe kansa.
Lauyar gwamnatin jahar Kano, Barista Wahida Isma’il, ta bukaci kotun ta bayar da damar karanto kunshin zargin kasancewar sabuwar takaddar tuhuma ce kuma kotun ta amince.
Bayan karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa nan ta ke ya musanta zargin.
Sai dai ya shaida wa kotun cewar ya yi hakan ne ba da niya ba, domin wani dan uwansu ne baya taimaka mu su, watakila idan yaji haka ya taimaka mu su.
Tunda fari dai rundunar yan sandan jahar Kano ce ta gurfanar da shi, bisa zarginsa da daukar Fetur a kwalaba da Ashana, inda yaje kusa kasuwar Dangoro ya yi yunkurin kunna wa kansa Wuta.
Kotun ta dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2024, don jiran shwarwarin gwamnati.
- Kotu Ta Tabbatar Da Abure A Matsayin Shugaban Jam’iyyar Labour
- A kan ƙarfin iko ne muke saɓani da Wike – Fubara