Wata babbar kotun Majistiri a jahar Ekiti ta bayar da umarnin tsare wasu mutane biyu da suka hada da, Kayode Seun da Godwin Festus , bisa zargin da laifin hada baki, Damfara da yunkurin bayar da cin hancin naira dubu dari hudu da tamanin da biyar N485,000 ga jami’an yan sanda.
Mai gabatar da kara ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su, wadanda suka amsa laifukan da ake zarginsu da aikata wa.
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa duk wanda aka samu da aikata laifin za a hukunshi sashe na 8 da 1 (3) uku cikin baka na dokar zamba 2006, sai sahse na 13 da 14 na laifukan yanar gizo-gizo 2015 da kuma sashe na 430 da 98A (b) cikin baka na dokokin kasa 2004.
An kama su ne a ranar 22 ga watan Afrilun 2024, da wata moto kirar Mercedes Benz CLA , wadda ake zargin ta sata ce, amma sai suka yi yunkurin bayar da cin hancin naira dubu dari hudu da tamanin da biyar N485,000 ga jami’an yan sandan amma suka ki karba.
Alkalin kotun mai shari’a ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni 2024, inda ya bayar da umarnin tsare su a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya.
- Yan Arewacin Nigeria Sun Nuna Rashin Amincewar Bai Wa Amurka Da Faransa Damar Kafa Sansani.
- Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Manajan Bankin FCMB Hukuncin Shekaru 121 Saboda Da Damfarar 112.1m