Kotu ta tura jami’in Binance gidan gyaran hali na Kuje

Spread the love

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da umarnin a tsare ɗaya daga cikin shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ƙarar ba da belinsa.

Alƙali Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin bayan da Gambaryan ya musanta tuhume-tuhumen halasta kuɗin haram da hukumar EFCC mai yaƙi da masuu yi wa arzikin ƙasa zangon ƙasa ke yi masa.

An gurfanar da Gambaryan gaban alƙali Nwite kan zargin aikata laifuka biyar.

Gambaryan ya kuma musanta tuhumar da aka yi cewa suna gudanar da harkokinsu ba tare da samun izini ba.

An gurfanar da shi tare da kamfanin Binance da Nadeem Anjarwalla wanda ya tsere.

Za dai a ci gaba da tsare shi har zuwa nan gaba a wannan watan na Afrilu. Ta kuma saka ranar 2 ga watan Matu domin ci gaba da shari’a.

EFCC ta shigar da ƙarar ne kan kamfanin Binance da Gambaryan da Anjarwalla wanda ya tsere daga Najeriya ranar 22 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *