Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta tura wasu daga cikin waɗanda suka gudanar da zanga-zangar tsananin rayuwa zuwa gidan yarin Kuje, bayan sun ƙi amsa tuhumar laifin cin amanar ƙasa.
A zaman kotun, mai shari’a Emeka Nwite ta bayar da umarnin a ajiye su har zuwa lokacin da za a saurari ƙara dangane da bayar da belin su a ranar 11 ga watan Satumba.
Mutanen da ake tuhumar dai sun musanta dukkan laifukan da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke tuhumar su da aikatawa guda shida da suka jiɓanci ta’addanci.