Kotun tarayya da ke zamanta a Maitama ta ƙi amincewa da belin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nema, inda ta bayar da umarnin a ajiye shi a gidan yarin Kuje.
Mai shari’a Maryann Anineh ta ce an yi gaggawar neman belin.
Yahaya Bello da wasu masu suna Abdulsalami Hudu da Umar Oricha ne suke fuskantar tuhuma kan zargin almundahanar kuɗi naira biliyan 110.4.
Hukumar EFCC ce ta yi ƙarar Yahaya Bello da sauran mutanen kan tuhume-tuhume 16 da suka haɗa cin amana da almundahana.
Sai dai kotun ta bayar da belin sauran waɗanda ake zargi tare da shi.