Wata Babbar kotun jihar kano ta baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar damar gudanar da zaben kananan hukumomi wanda aka shirya gudanarwa ranar asabar 26 ga watan October.
Sai dai a umarnin da Babbar kotun jihar kano karkashin jagorancin mai Shari’a Sanusi Ma’aji a yau juma’a a baiwa hukumar umarnin cigaba da shirye-shiryen zaben domin ganin an gudanar da zaben a gobe asabar.
Hukumar zaɓe mai zaban kanta ta jihar kano ce dai ta shigar da karar inda take karar jam’iyyar APC da wasu guda 13.
Kamar yadda mai Shari’a Ma’aji ya bayyana hukumar zaben ta jihar kano tana da ikon shiryawa da kuma gudanar da zaben kananan hukumomi 44 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata dama.
Ya ce yayi watsi da duk wani yunkuri na kawo wa zaben cikas.
Kotun ta kuma umarci dukkanin jami’an tsaro dake jihar da su tabbatar sun samar da tsaro yayin zaben kananan hukumomin na jihar kano.
a ranar talata wata Babbar kotun tarayya dake kano ta rushe shugabanni hukumar Zaɓen tare da bukatar samar da sabbi wadanda suka chanchanta domin gudanar da zaben.
KADAURA24