Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a Akure ta umurci majalisar dokokin jihar da ta kafa kwamitin da zai binciki halin da lafiyar gwamna Rotimi Akeredolu ke ciki.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan dawowar sa daga hutun jinya a ƙasar Jamus wata shida da suka gabata, gwamnan ya tare a Ibadan babban birnin jihar Oyo domin ci gaba da kula da lafiyarsa.
Wannan ne ya zaburar da al’umma jihar ke neman a gudanar da bincike kan lafiyarsa.
Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya aiko ma na da wannan rahoto.