Babbar kotun shari’ar addinin musulinci mai namba 1 Fagge Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Umar lawan Abubakar, ta umarci jami’an yan sandan jahar , da su tabbatar duk lokacin da aka kama Yan Daba ma su dauke da muggan makamai, su binciko ma su kerawa ko kuma siyar musu da makaman don a sanya su cikin tuhumar.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa odar na zuwa ne, bayan kotun ta yanke wa wani matashi mai suna Yusuf Muhummed, hukuncin daurin shekaru uku a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya ba tare da zabin biyan tara ba.
Yan sanda ne suka gurfanar da shi, bisa zarginsa da fito da wuka ya kwace wayar wata mata amma jama’ar gari suka yi nasarar kama shi.
Kotun ta ce, tun daga kan mataimakin sufeton yan sandan Nigeria dake kula da shiya ta daya wato zone one, kwamishinan yan sanda, mataimakan kwamishinan yan sanda da kuma baturen yan sanda, da sauran hukumomin tsaron jahar, duk wanda aka samu da muggan makamai da zai haifar da rudani ga al’umma ko tayar da hankalinsu, har da ma su kerawa zuwa siyarwa suna da damar kama su, domin gurfanar da su a gaban kotu mai hurumi.
- Za a rataye mutane 3 kan kisan kwamandan soji
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Tabbatar Da Rasuwar Jami’an Ta 5 Wasu 10 Suka Jikkata.
Odar kotun mai kwanan watan 20 ga watan Satumba 2024, ta ce wannan odar ta fara aiki ne tun daga ranar 27 ga watan Augustan 2024.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daman kamawa, bincike da kuma gurfanar da yan daba harma da ma su kerawa ko siyarwa aikinsu kuma za su ci gaba.
Sai dai ya ce umarnin kotun ya kara karfafa mu su gwiwa , domin duk wanda suka kama sai sunyi bibiyar zakulo inda ake kerawa ko siyarwa, don harkar daba da kwacen waya ta ishi kowa a jahar.
Saurari Muryar Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Mai magana da yawun manyan kotun shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa tuni lauyoyi suka yi na’am da umarnin alkalin da kuma yin kira ga gwamnatin jahar, don kai batun majalissar dokokin jahar , a yi dokar sanya idanu kan wadanda suke kera makaman da kuma siyarwa.
saurari murayar Kakakin manyan kotunnan shari’ar musulinci na Kano Muzammil Ado Fagge