Babbar kotun tarayya a Abujan Najeriya ta wanke shugaban ƙugiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bello Bodejo, daga zargin aikata ta’addanci da gwamnatin ƙasar ke yi masa.
Cikin wani taƙaitaccen hukunci da Daily Trust ta ruwaito ta bakin kamfanin dillancin labarai na NAN, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya wanke shi ne bayan lauyar ministan shari’a na Najeriya, Aderonke Imana, ta nemi janye tuhuma uku da suke yi masa.
Lauyar ta faɗa wa alƙalin cewa Ministan Shari’a Lateef Fagbemi ne ya umarce ta ta janye ƙarar “bisa adalci”.
Ahmed Raji, wanda shi ne lauyan Badejo, bai ƙalubalanci ƙudirin janye tuhumar ba.
Tun a watan Maris da ya gabata a gabatar da Bodejo a gaban kotun bisa zargin aikata ta’addanci bayan ya kafa wata ƙungiyar ‘yan sa-kai a jihar Nasarawa.
- Tinubu ya samu tarba da sabon taken Najeriya a majalisar dokokin ƙasar
- Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya na son a binciki lauyoyin Sanusi da Aminu Ado