Kotun majistiri Mai namba 51 dake zaman ta , a rukunin kotuna na Norman’Sland Kano , ta yanke hukuncin daurin shekaru shida-shida akan wasu mutane 2 da suka hada da Muray Mopolo da kuma Ndike Ekwe, bisa Samun da laifin hadin Baki don aikata laifi, Mallakar Bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma siyar da Ita.
Mai gabatar da kara Barista Abdussalam Dan-Maidaki , ya bukaci kotun a karanto mu su , kunshin tuhume-tuhumen da ake Yi mu su.
Kotun ta ba wa jami’in ta Nazir Damisawa, umarnin karanto mu su , kuma bayan an karanta mu su , sun amsa laifukan da ake tuhumar su.
- Matar ɗan majalisa na shan suka kan neman matasa su yi sana’ar sayar da rake.
- Mun kashe Halilu Sububu saura Bello Turji da sauran ƴan ta’adda – Janar Musa
Mai shari’a ta kotun majistirin Mai namba 51, Hajara Safiyo Hamza, ta yanke mu su hukuncin daurin shekaru bibiyu kan kowanne laifi wato kowannensu zai shafe shekaru Shida a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.
Sannan kuma za su biya naira Dubu hamsin- hamsin kan kowanne laifi.
Tun a shekarar 2023 aka kama Muray Mopolo mazaunin unguwar Bompai Kano da kuma Ndike Ekwe mazaunin unguwar Sabon Gari.