Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Da Bulala 150 Ga Wanda Aka Samu Da Laifin Kunnawa Mutane Wuta A Masallaci

Spread the love

Babbar kotun shari’ar addinin Muslunci dake zaman, a unguwar Danbare Kano, ta yankewa matashin nan Mai suna, Shafi’u Abubakar, Dan shekaru 38 Mai sana’ar Adaidaita sahu, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa samunsa da laifin kisan Kai , ta hanyar 23 mutane wuta lokacin da suke yin sallar asuba a Wani masallaci dake Garin Gadan, karamar hukumar Gezawa Kano.

A lokacin da kotun take yin waiwayen baya kan shaidun da aka gabatar , ta yi watsi da shaidu 5 cikin shaidu 7 da lauyoyin Gwamnatin jihar Kano, suka gabatar da saboda rashin ingancinsu, Inda kotun ta karbi shaidu guda biyu.

Da yake yanke hukuncin Mai shari’a Halhalatul Kuza’i Zakariya, ya yankewa Shafi’u Abubakar, hukuncin kisa ta hanyar rataya a laifi na farko tare da umartar gwamnati ta karbe Baburin Adaidaita sahunsa , a siyar dashi don gyara masallacin da ya Kona .

A laifi na biyu kuma kotun ta yanke masa hukuncin Bulala 100, laifi na Uku an Yi masa tarar naira duba Daya da dari biyar 1500, sai laifi na hudu kuma Bulala 50.

Shaidun da kotun ta karba sun hada da na jami’in Dan Sandan da ya gudanar da bincike da kuma na daya daga cikin Wadanda ya tsallake rijiya da baya bayan kunna musu wuta a cikin masallacin, Inda kotun ta karbi shaidu biyu.

Kuma likitoci sun tabbatar da rasuwar mutane 23 da aka kwantar a asibitin kwararru na Murtala Muhammed.

Kotun ta ce ta samu Shafi’u Abubakar, da laifukan 4 da suka hada Barna ta hanyar kunna wuta, sanadiyar Samar da rauni , kisan Kai da gangan.

Idan ba a manta, lamarin ya faru ne a ranar Laraba 15 ga watan Mayu 2024, a yankin Gadan dake Karamar hukumar Gezawa Kano.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ya fitar bayan faruwar lamarin ya ce sun samu kiraye-kirayen jama’a kan cewar wuta ta tashi da misalin karfe 5:20am na Asuba, a wani masallaci dake kauyen Gadan Karamar hukumar Gezawa, a daidai lokacin da suke yin sallar Asuba, wadanda mutane da dama Suka samu ranuka.

Bayan samun rahotan ne Kwamishinan Yan Sandan Kano , ya tura wasu jami’an yan sanda , wadanda Suka kware kan duk wani Abu da yake tashi kamar Abun fashewa da dai sauransu, karkashin jagorancin CSP Haruna Isma’il, da kuma Baturen yan sanda na Gezawa CSP Haruna Iliya, tare da ba su umarnin a gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru, dan ganin an yi abunda yakamata.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa, bayan sunje wajen ne , aka samu nasarar toshe ko’ina ,tare da gaggauta ceto mutane 24, inda aka garzaya da su Babban asibitin kwararru na Murtala Muhammed, a Birnin Kano.

Sai a ranar 19 ga watan Mayun 2024 kakakin yan sandan , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya  ce mutane 24, da aka kwantar a asibitin Murtala Muhammed, 17 sun mutu.

Binciken yan sanda na farko-farko, ya tabbatar da cewar, an jefa wuta ne ta Hanyar amfani da man Fetur.

Rundunar ta kara da cewa wanda ake zargi na farko mai suna Shafi’u Abubakar, an Kama shi, kuma ya tabbatar da cewa shi ne yaje ya siyo man Fetur a gidan mai, sannan ya sanya a cikin Wata roba ya watsa a cikin masallacin ya kunna wuta.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya faru ne sakamakon rigimar cikin gida.

A ranar 20 ga watan Mayun 2024 , kakakin manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jihar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya sanar da cewa za a gurfanar da matashin, a gaban babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Rijiyar Zaki,  karkashin jagorancin mai Shari’a Halhalatul Kuza’i Zakariya.

 

Haka zalika a ranar 20 ga watan Mayu 2024, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin daukar matakin Shari’a, kan matashin mai suna, Shafi’u Abubakar, da ake zargi da bankawa jama’a wuta a lokacin da suke yin sallar Asuba, a yankin Unguwar Gadan dake Karamar hukumar Gezawa Kano, inda mutane 24 Suka kone sakamakon Iftila’in.

Gwamnan Abba Kabir, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano, don duba wadanda Suka gamu da iftila’in konewar.

Gwamnan ya yi Allah Wadai da yadda matashin ya Rufe jama’a suna yin sallah, sannan ya banka mu su wuta, inda ya tabbatar da gwamnati ba za ta kyale lamarin ba.

Abba Kabir Yusuf, ya nesanta batun da siyasa ko ta’addanci, kamar yadda wasu ke fada , harma ya bayyana cewa rigimar cikin gida ce ta rabon gado, sakamakon wani bai ji dadi ba, ya yanke wa kansa hukunci irin na marasa imani.

” Don in banda Kafiri , Wanda Allah ya tsinewa albarka babu Wanda zai zo ya yi wannan ta’addanci shi akansa ya kone bayin Allah” Gwamna Abba K Yusif’’.

 

A lokacin ziyarar tawagar gwamnan Kanon ta hada da Kwamishinan yan aandan jihar Kano, da Darektan hukumar tsaron farin kaya DSS reshen jahar Kano, da kuma sauran mukarraban gwamnati.

An gurfanar da matashin da zargin  aikata laifuka hudu da suka hada da,  kisa da Yunkurin aikata kisa, Samar da mummunan rauni da kuma barnata dukiya wanda ya saba da sashe na 140, 148, 167 da kuma 370 Inda matashin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

 

Lauyoyin gwamnati kuma masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu 7 da suka hada da Dagacin garin Gadan, da yayan wanda ake zargi da kuma kaninsa.

A jawabinsa, shaida na farko wanda kuma shi ne Dagacin garin Gadan, Malam Abdulazeez Yahaya, ya shaida wa kotun cewa kiran sa aka yi aka sanar da shi halin da jama’arsa suka samu kansu a cikiin.

Daga nan suka yi kokarin garzayawa da su babban Asibitin Sir Sanusi da ke Yankaba, kafin daga bisani aka mayar da su Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed.

Da yake bayar da shaida, shaida na biyu wanda kuma yaya ne ga Shafiu, wato Aminu Abubakar, ya bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da Shafiu ya fara aikata irin wannan daba’ira ba.

A cewarsa, a shekarun baya ya taba farfasawa kawunansa kai, lamarin da ya janyo aka kai shi Asibitin Masu Lalurar Kwakwalwa da ke Dawanau don gwada kwakwalwarsa, inda aka tabbatar da cewa ba shi da wata matsala ta tabin hankali, kamar yadda ake zato.

“Sai dai an ba mu shawara cewa mu nemar masa aikin yi, anan ne mahaifiyarmu ta sa muka sayar mata da gonarta Naira dubu dari 350 ta nemi mu yafe wa Shafiu don ya fara sana’a da kudin, inda ya sayo Adaidaita Sahu ,mai ya ci gaba da harkokinsa.”

Haka zalika ma su gabatar da karar sun gabatar da wani jami’in dan sanda mai suna ASP Abdullahi Sajau, da ya jagoranci gudanar da binciken da ake yi wa Shafi’u Abubakar, bayan jami’an yan sandan Gezawa sun mika shi, babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan Kano.

ASP Abdullahi Sajau, ya shaida wa kotu cewa ‘’ sun ziyarci asibitin Murtala Muhammed, inda suka tarar da da mutane 25 wadanda suka gamu da iftila’in , kuma ana zargin shafi’u ne ya kona su bayan ya siyo man fetur na naira dubu bakwai ‘’.

A bayanansu daban-daban, kannen wanda ake zargi Shuaibu Ibrahim da Ibrahim Sani sun bayyana cewa suna tsaka da Sallah suka ji tashin wuta a masallaci inda suka yi waje da gudu, wuta tana ci a jikinsu, lamarin da ya janyo suka sami raunuka a jikinsu.

Sai dai, ita kuma a nata bangaren, lauyar dake kare wanda ake tuhumar , Barista Asiya Muhammad Imam, ta yi wa shaidun ma su kara tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *